23 Yuli 2019 - 04:30
​An Sake Dage Zaben 'Yan Majalisa A Kamaru

A Karo na biyu shugaban kasar Kamaru ya sake dage zaben 'yan Majalisar Dokokin kasar wanda ya kamata a gudanar a shekarar bara zuwa shekarar 2020

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto shugaban kasar Kamaru Paul Biya cikin wani kudirin da ya fitar, ya yi karin wa'adin shekara guda da watanni biyu ga 'yan Majalisar dokokin kasar wanda hakan ke nufin cewa a dage gudanar da zaben 'yan Majalisar zuwa shekarar 2020 mai kamawa.

Kafin hakan dai shugaban ya dage zaben 'yan Majalisar jihohi da ya kamata a gudanar a shekarar da ta gabata zuwa karshen wannan shekara ta 2019 da muke ciki.

Majiyar Majalisar ta Kamaru ta bayyana cewa Shugaba Paul biya ya dauki wannan mataki ne domin rage yawan kudaden da ake kashewa a lokutan zabe.

A halin da ake ciki yanzu, kasar ta Kamaru na fuskantar matsalolin tsaro, kama daga na kungiyar Boko haram a arewacin kasar da kuma na 'yan aware masu amfani da turancin Ingilishi a arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar.

A bangare guda kuma ga rikicin siyasa, inda 'yan adawa suka yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar na shekarar bara, bayan da suka zargi gwamnati da tabka magudi tare da kiran magoya bayansu da gudanar da zanga-zanga a fadin kasar.



/129